logo

HAUSA

Faraministan Nijar ya yi tsokaci kan matakin da gwamnatin Benin ta dauka na hana wucewa da dayen man fetur din Nijar

2024-05-13 09:46:03 CMG Hausa

A ranar Asabar 11 ga watan Mayun shekarar 2024, a yayin wani taron manema labarai a fadar faraminista dake birnin Yamai, Ali Mahamane Lamine Zeine, faraministan Nijar ya yi tsokaci kan matakin kasar Benin na hana wucewa da gurbataccen man fetur din kasar Nijar daga tashar ruwa ta Seme-Kpodji da ke kasar Benin.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

A yayin wannan taron manema labarai da ya gudana gaban idon mambobin gwamnatin wucin gadi da na kwamitin ceton kasa na CNSP, da manyan mashawartan fadar da faraminista da kuma ’yan jarida na gida da waje, shugaban gwamnatin Nijar, Ali Mahamane Lamine Zeine ya fara da batun bututu dake kai man fetur din Nijar daga kauyen Koulele a kasar Nijar zuwa Seme a kasar Benin, akwai yarjejeniyoyi gomai da aka sanyawa hannu domin ganin an kawar da duk wasu matsaloli da za su hana malalar wannan gurbataccen har inda za shi, ko wata dama ko wani dalili da za su hana burin da aka cimma na kafa wannan bututu, sai dai dukkan wadannan yarjejeniyoyi hukumomin kasar Benin sun sa kafa, sun  take su. Amma, za mu karanta na layi guda na abin da wadannan yarjejeniyoyi suka tanada, in ji faraministan Nijar, shi ne gwamnatin Benin ba za ta canza, ba za ta soke, ba za ta tsaida, ba za ta sanarwa da cewa akwai kasawa ba, ko kuma tilastawa, ko kuma neman kaucewa ko kuma takaitawa ta kowane hali wadannan yarjejeniyoyi da aka shimfida kuma aka sanyawa hannu, sannan kuma idan ana neman kafa wasu takardun tsare-tsare, da kuma na neman kudi, dole sai an shaida wata amincewa a rubuce, domin nuna muku cewa bisa ga wadannan tanade-tanade, kasar Benin ba ta da ikon hana man fetur din Nijar wucewa ta kasarta, domin ya shafi ratsa teku da zuwa kasuwar duniya.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.