NATO ta yi atisayen sojan laima a dab da iyakar Rasha
2024-05-13 14:23:58 CMG Hausa
Daga ran 11 zuwa 12 ga wannan watan, mambobin kungiyar tsaro ta NATO sun yi atisayen sojan laima a kasar Estonia dake dab da iyaka da kasar Rasha, wanda wani bangare ne na atisayen soja mai taken “Mai tsaro dake da karfin zuciya na shekarar 2024” wato Steadfast Defender 2024 a turance.
Rahotanni na cewa, an gudanar da wannan atisayen soja a wurin dake dab da iyakar Rasha, wanda sojojin Birtaniya da Amurka 142 suka yi hadin gwiwa wajen gabatar da shi.
Za a gudanar da atisayen har zuwa karshen wannan watan da muke ciki, wanda ya kunshi sojoji kimanin dubu 90, a wuraren dake gabashin NATO, dake dab da iyakar Rasha.
Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta shedawa manema labarai cewa, manufar NATO ita ce dakile Rasha, abin da ya bayyana takarar da suke yiwa da Rasha, wanda kuma zai tsananta halin da ake ciki. (Amina Xu)