logo

HAUSA

Li Qiang ya taya Mikhail Vladimirovich Mishustin murnar sake zama firaministan Rasha

2024-05-13 13:07:40 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya aike da sako ga Mikhail Vladimirovich Mishustin, don taya shi murnar sake zama firaministan kasar Rasha.

Li Qiang ya bayyana cewa, karkashin jagorancin manyan tsare-tsaren da shugaban Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Vladimirovich Putin suka yi, dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare ta sabon zamani daga dukkan fannoni tsakanin kasashen biyu ta ci gaba da karuwa lami lafiya. Ya kara da cewa, bangarorin biyu na kara samun amincewar juna ta fuskar siyasa, da habakar hadin gwiwar moriyar juna yadda ya kamata, da kuma kara mu’amala a fannin al’adu, wadanda suka kawo ainihin alheri ga kasashen biyu da ma al’ummunsu baki daya. 

Har ila yau, Li Qiang ya ce yana fatan ci gaba da kokari da firaminista Mishustin don ba da sabuwar gudummawa wajen karfafa dangantaka da hadin gwiwa mai amfani tsakanin  kasashen Sin da Rasha.(Safiyah Ma)