logo

HAUSA

Babban sakantaren MDD ya sake nanata wajibcin dakatar da bude wuta a zirin Gaza

2024-05-13 10:52:30 CMG Hausa

 

Babban sakataren MDD António Guterres da sauran hukumomin majalisar, sun sake nanata wajibcin tsagaita bude wuta a zirin Gaza, tare da kira da a yi la’akari da barazanar jin kai da ake fuskanta a wurin, duba da yadda sojojin Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare.

Antonio Guterres ya bayyana jiya a Kuwait cewa, rikicin da ya dade yana addabar al’ummar zirin Gaza ya haifar da babbar barazana, lamarin da ya kai dimbin fararen hula ga rasa gidajensu. Ban da wannan kuma, ya sake yin kira ga bangarorin masu ruwa da tsaki da su saki mutanen da suke tsare da su tare da dakatar da bude wuta.

A wannan rana kuma, ofishin manyan jami’an MDD mai kula da harkokin hakkin Bil Adama ya bayyana matukar damuwa kan yadda yanayin keta hakkin Bil Adama a zirin Gaza ya kara tsananta cikin sauri, inda ya ce matakin da Isra’ila ke dauka na tilasta tarwatsa fararen hula da kaiwa wuraren taruwar jama’a da dama hare-hare, sun saba da dokar kare hakkin Bil Adama da hukunci mai alaka da kotun kasa da kasa ta yanke. (Amina Xu)