logo

HAUSA

Kenya: An Kammala Baje Kolin Harkokin Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Afrika

2024-05-12 15:50:18 CMG Hausa

An kammala taron baje kolin harkokin raya tattalin arziki da cinikayya na kasar Sin da kasashen Afirka ko CAETE, na shekarar nan ta 2024 a birnin Nairobin kasar Kenya, inda mahalarta suka sabunta kira da a kara habaka dangantakar kasuwanci tsakanin Sin da Afirka.

Pius Rotich, babban manajan sashen bunkasa zuba jari da raya harkokin kasuwanci na hukumar kula da harkokin zuba jari ta kasar Kenya, ya ce baje kolin ya samarwa kamfanonin kasar Sin dandalin kulla dangantaka da takwarorinsu dake fadin nahiyar Afrika.

Ya ce, suna fatan dangantakar da aka kulla yayin baje kolin za ta bunkasa cinikayya tsakanin bangarorin biyu.

Shi kuwa Gao Wei, manajan daraktan kamfanin shirya baje koli na Afripeak dake Kenya, wanda daya ne daga cikin mashirya taron, ya ce baje kolin ya karawa ‘yan kasuwar Afirka dake da burin kulla dangantaka da kamfanonin kasar Sin kwarin gwiwa.

Yayin baje kolin, an cimma akalla yarjejeniyoyin cinikayya 10, tsakanin kamfanonin Sin da na Afrika, cikin har da wadanda suka shafi shirin kafa cibiyar sarrafa man furen Sunflower ta kasar Tanzania da shirin gina wuraren ajiye kayayyaki a kasar Djibouti, wanda kamfanin jigilar kayayyaki na Yongzhou zai aiwatar da kuma shirin hadin gwiwa kan cinikayyar busasshen kifi na kasar Kenya. (Fa’iza Mustapha)