Kasar Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Zuwa Sararin Samaniya
2024-05-12 15:58:46 CMG Hausa
Da safiyar yau Lahadi, rokar Long March-4C ta harba sabon tauraron dan Adam na kasar Sin zuwa sararin samaniya
Rokar ta tashi ne da misalin karfe 7:43 na safe agogon Beijing, daga cibiyar harba taurarin dan Adam ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin, inda ta harba tauraron Shiyan-23 zuwa falakinsa kamar yadda aka tsara.
Za a iya amfani da tauraron ne musammam domin bibiyar yanayin muhallin sararin samaniya.
Wannan shi ne karo na 522 da aka yi amfani da jerin rokar Long March wajen aiwatar da irin wannan aiki. (Fa’iza Mustapha)