Isra’ila ta bayar da sabon umarnin kwashe mutane daga Rafah bayan MDD ta kada kuri’ar amincewa da kasancewar Palasdinu mambarta
2024-05-12 16:24:10 CMG Hausa
Isra’ila ta bayar da sabon umarnin kwashe mutane daga birnin Rafah dake kudancin Gaza, yayin da take shirin fadada ayyukan soja a birnin, kwana guda bayan MDD ta zartas da kudurin da ya amince da bukatar Palasdinu ta zama cikakkiyar mamba a majalisar.
Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar sojan Isra’ila Avichai Adraee, ya ce wajibi ne mazauna sansanonin ‘yan gudun hijira na Shaboura da Al-Adari da Al-Jeneina da kewayen Khirbbet Al-Adas dake rukunan gine-gine na 6-9 da 17 da na 25-27 da na 31, su bar gidajensu nan take.
A cewarsa, mayakan Hamas na amfani da wadannan wurare wajen kai hare-hare kan mutanen Isra’ila, lamarin da ya tilastawa rundunar sojin ta Isra’ila fadada ayyukanta domin dakile mayakan na Hamas.
A ranar Juma’a ne MDD ta amince da wani muhimmin kuduri na mara baya ga yunkurin Palasdinu na zama cikakkiyar mambarta.
Wannan ya nuna karuwar goyon bayan ga al’ummar Palasdinu, bisa la’akari da yadda kasashe da dama suka bayyana fushinsu ga karuwar mace-macen mutane a Gaza da kuma damuwarsu kan yiwuwar Isra’ila ta kaddamar da mummunan farmaki a Rafah.
Kudurin ya samu kuri’un amincewa 143 da na rashin amincewa 9, ciki har da Amurka da Isra’ila, yayin da kasashe 25 suka kaurace wa kada kuri’ar. Wannan na tabbatar da Palasdinu ta cancanci zama cikakkiyar mamba daga kasancewarta ‘yar sa ido. (Fa’iza Msutapha)