logo

HAUSA

‘Yan bidiga sun yi awon gaba da daliban jami’ar jihar Kogi dake yankin tsakiyar Najeriya

2024-05-11 16:34:18 CMG Hausa

Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da daliban jami’ar kimiyya da fasaha ta jihar Kogi, dake shiyyar tsakiyar tarayyar Najeriya, bayan da suka kai farmaki harabar jami’ar dake yankin karamar hukumar Okene, inda suka rika bude wuta tare da tusa keyar wasu daga cikin daliban.

Mataimakin shugaban jami’ar Abdulrahman Asipita, ya shaidawa manema labarai cewa, maharan sun kutsa a kalla dakunan gabatar da darussa 3 dake cikin jami’ar a daren ranar Alhamis, yayin da rukunonin dalibai daban daban ke bita, gabanin fara jarrabawa a Litinin mai zuwa. Asipita ya ce yanzu haka komai ya lafa, kuma mahukunta na daukar dukkanin matakan da suka kamata.

A daya bangaren, cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin gwamnatin jihar ta Kogi Kingsley Fanwo, ya ce kawo yanzu kimanin dalibai 9 ne aka samu rahoton bacewar su. Ya ce “Gwamnatin jihar tana aiwatar da matakan tsaro na bibiyar maharan don kama su, da tabbatar da an kubutar da daliban da aka sace.” (Saminu Alhassan)