Shugaba Xi ya jaddada muhimmancin cimma sabbin matakai a fannin yada ilimin akidu da siyasa
2024-05-11 21:15:01 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin kara azama, wajen ci gaba da cimma sabbin matakai a fannin yada ilimin akidu da siyasa a makarantu a sabon zamani. Shugaba Xi, ya yi kiran ne cikin umarnin da ya bayar game da gina kwasa-kwasai masu nasaba da hakan a makarantun kasar Sin.
Ya ce abu ne mai matukar muhimmanci a samar da tsarin littattafan karatu masu mayar da hankali ga gina salon tunanin gurguzu mai halayyar musamman ta Sin a sabon zamani, da dunkule ilimin siyasa a dukkanin matakan ilimi, tun daga makarantun firamare har zuwa jami'o'in kasar. (Saminu Alhassan)