logo

HAUSA

Firaministan Sin ya jaddada bukatar inganta dukkanin matakan samar da ci gaba ta hanyar kirkire-kirkire

2024-05-11 20:55:50 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya jaddada bukatar gaggauta samar da sabon karfin sarrafa hajoji, da inganta zarafin samar da ci gaba ta hanyar kirkire-kirkire.

Li Qiang wanda ya yi kiran a jiya Jumma’a, yayin da yake ziyarar gani da ido, da bincike a lardin Anhui dake gabashin kasar Sin, ya ce Sin za ta ci gaba da zuba jari a muhimman fannonin bincike, da tallafawa ci gaban kirkire-kirkire.

Ya ce alfanun kimiyya da fasaha na kunshe cikin cin gajiyar aiwatarwa, da amfanar da bil adama. Don haka firaminista Li ya yi kira da a zurfafa sauye-sauye, da nufin karkatar da gajiyar da ake ci daga ilimin kimiyya da fasaha zuwa karfin sarrafa hajoji na hakika. (Saminu Alhassan)