logo

HAUSA

Antonio Guterres ya yi kira da a aiwatar da matakan dakile sauyin yanayi da tashe tashen hankula a Afirka

2024-05-11 17:31:02 CMG Hausa

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya sake yin kira ga sassan kasa da kasa, da su goyi bayan matakan dakile kara tabarbarewar yanayi, da tashe tashen hankula, wadanda ke gurgunta fatan da ake da shi na samar da tsaro, daidaito da dorewar ci gaba a nahiyar Afirka.

Mista Guterres ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai, a gefen taron jam’iyyun gama kai na MDD, wanda aka kammala a jiya Jumma’a a birnin Nairobin kasar Kenya. A cewarsa, nahiyar Afirka ta zamo cibiyar dake fama da yanayin gaggawa game da sauyin yanayi, duk da kasancewar abubuwan da take fitarwa, masu haifar da mummunan tasirin yanayi ba su kai sun kawo ba.

Babban jami’in na MDD, ya jaddada cewa, Afirka na iya shawo kan kalubalen sauyin yanayi, da zarar nahiyar ta karbi rabon ta na jarin makamashi da ake iya sabuntawa, da sauran matakan jure tasirin sauyin yanayi.

Har ila yau, Guterres ya jaddada cewa, MDD za ta kara matsa kaimi ga batun tabbatar da adalci ga kasashen Afirka, don gane da batun sauyin yanayi, inda ya ce a gwamman shekarun baya bayan nan, kaso 2 bisa dari kacal nahiyar ta samu, cikin jimillar jarin makamashi mai tsafta da ya kamata a samar gare ta.

Daga nan sai ya yi kira ga manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki, da su cika alkawuran su, na samar da kudaden yaki da sauyin yanayi a Afirka, yayin da kuma suke fadada karo-karo da suke shigarwa cikin sabon asusun da aka kafa, na magance asara da lalacewar yanayi. (Saminu Alhassan)