An bude sabuwar tashar fiton kaya a garin Funtua ta jihar Katsina a arewacin Najeriya
2024-05-11 15:05:37 CMG Hausa
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da aiki a sabuwar tashar fiton kaya a yankin karamar hukumar Funtua dake jihar Katsina a arewacin Najeriya.
Ita dai wannan tasha za ta taimakawa ’yan kasuwa wajen daukar kayan da suka yiwo oda ba tare da sun je tashar bakin teku ba, musamman ’yan kasuwar dake arewacin kasar
da suke da tazara da bakin ruwa.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
An dai kaddamar da tashar ce a ranar Alhamis 9 ga wata.
Shugaban tarayyar Najeriya wanda ya sami wakilcin sakataren gwamnatin tarayyar Mr. George Akume, ya ce, tashar ita ce irinta ta uku da aka kammala a kasar daga cikin guda shida da gwamnati ta tsara ginawa.
Ya ce, babu shakka dai sabuwar tashar fiton kayan ta Funtua za ta saukaka harkokin hada-hadar kasuwancin kasa da kasa musamman ma ga ’yan kasuwar da suke shigo da kaya ko fitarwa ta amfani da sufurin jiragen ruwa.
Shugaba Tinubu ta bakin sakataren gwamnatin tarayyar ya ce, babban abin farin cikin yanzu ’yan kasuwar Najeriya da kasashe makwafta kamar jamhuriyyar Nijar da Kamaru da Chadi za su sami rangwame sosai wajen tantance kayayyakin da suke yiwo oda ba tare da daukar wani dogon lokaci ba.
“Wannan sabuwar tashar fiton kayan tana da matukar muhimmanci ga kokarin gwamnati na bunkasa sha’anin fita da shigo da hajoji daga waje wanda hakan kuma zai kawo daidaito ga harkokin cinikayya a Najeriya.”
A jawabinsa gwamnan jihar Katsina Alhaji Dikko Radda yabawa gwamnatin tarayyar ya yi bisa kokarin da ta yi wajen tabbatar da kammaluwar aikin tashar.
“Wannan aiki hakika zai saukaka hada-hadar sufurin kayayyaki tare kuma da rage yawan asara da ’yan kasuwa ke yi a duk lokacin da suka sami jinkiri na dauko kayayyakinsu daga bakin teku sabo da tsauraran matakan da ake bi na tsawon lokaci a hukumance kafin ’yan kasuwa su samu damar dauko kayan da suka yiwo oda zuwa arewacin Najeriya.” (Garba Abdullahi Bagwai)