Sin ta goyi bayan kudurin kwamitin tsaron MDD na sake gaggauta duba yiwuwar amincewa da bukatar Falasdinu ta zama mamba a MDD
2024-05-11 17:11:05 CMG Hausa
Kasar Sin ta goyi bayan kudurin kwamitin tsaron MDD, na sake gaggauta duba yiwuwar amincewa da bukatar Falasdinu, ta zama mamba a MDD. Da yake tabbatar da hakan cikin jawabin da ya gabatar a jiya Jumma’a, yayin zaman gaggawa na babban taron MDD karo na 10, wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya jaddada bukatar baiwa Falasdinu matsayin cikakkiyar mamba a MDD.
Fu Cong ya ce “Ya kamata falasdinu ta samu matsayi guda da Isra’ila, kuma nauyi ne a wuyan sassan kasa da kasa, su goyi baya, da ingiza matakan kafuwar kasar Falasdinu mai cin gashin kai, don tabbatar da an aiwatar da tsarin warware matsalar yankin ta hanyar kafa kasashe biyu, da wanzar da zaman lafiya mai dorewa a gabas ta tsakiya”
Game da yanayin da ake ciki a baya bayan nan, Fu ya bayyana rashin jin dadi, bisa yadda Amurka ta ki amincewa da kudurin da aka gabatar na baiwa Falasdinu damar zama cikakkiyar mamba a MDD, yayin jefa kuri’un da aka kada a zauren kwamitin tsaron MDD a ranar 18 ga watan Afrilun da ya shude.
Jami’in ya soki lamirin Amurka, bisa yadda ta yi amfani da matsayin ta na mai kujerar naki, wajen dakile damar tarihi ta sauya rashin adalcin da aka yiwa Falasdinawa, yana mai cewa, “matakin ya saba da nauyin dake wuyan wata kasa babba.”
Zaman taron gaggawa na babban taron MDD, bisa babban rinjaye, ya zartas da kudurin dake kara jaddada hakkin al’ummar Falasdinawa na cin gashin kai, da tabbatar da dacewar Falasdinu, na zama cikakkiyar mamba a MDD, da shawartar kwamitin tsaron ya sake duba bukatar ta Falasdinu. (Saminu Alhassan)