Babban taron MDD ya yanke shawarar baiwa Palasdinu karin iko a majalisar
2024-05-11 15:58:26 CMG Hausa
A jiya Juma’a aka koma zaman taron gaggawa na babban taron MDD karo na 10, inda aka zartas da kudurin baiwa Palasdinu karin iko a majalisar. Bisa kuri’u da aka kada, kudurin ya shawarci kwamitin sulhu da ya sake tantanci Palasdinu, da nufin shigar da ita majalisar a matsayin mamba, bisa la’akari da halin da duniya ke ciki.
An zartas da wannan kuduri bisa kuri’un amincewa 143, da na kin amincewa 9, yayin da mambobi 25 suka ki jefa kuri’un su. Amurka da Isra’ila sun jefa kuri’un kin amincewa da kudurin.
Kafin kada kuri’un, shugaban babban taron Dennis Francis ya bayyana cewa, rikicin Palasdinu da Isra’ila ya addabi duniya a tsawon fiye da shekaru 70, kuma ci gabansa a baya bayan nan ya nuna cewa, dole ne a magance wannan matsala ba tare da bata lokaci ba.
Mista Francis ya kuma yi kira ga mambobin da su kimanta halin da ake ciki, da taka rawar gani wajen kokarin shimfida zaman lafiya a duniya, kana ya yi kira ga mambobin da su mutunta MDD da babban taronta, yayin da suke gabatar da jawabi. (Amina Xu)