Xi Jinping ya halarci bikin ban kwana da firaministan Hungary ya shirya masa
2024-05-10 23:06:53 CMG Hausa
Da tsakar ranar yau Jumma’a ne, agogon wurin, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da uwargidansa Peng Liyuan, suka halarci bikin ban kwana da su da firaministan kasar Hungary gami da uwargidansa suka shirya musu a birnin Budapest.
Firaministan Hungary, Viktor Orban ya gabatar wa shugaba Xi tarihin birnin Budapest, da ci gabansa gami da yadda za’a tsara fasalinsa a nan gaba, inda a cewarsa, kamfanonin kasar Sin sun bayar da muhimmiyar gudummawa ga ci gaban tattalin arziki da bunkasuwar biranen Hungary. Ya ce fasahohin kasar Sin na sahun gaba a duniya, kuma Hungary na fatan fadada hadin-gwiwa da kasar Sin, da kara da shigar da fasahohin zamani na kasar, a wani kokari na raya kasa da kyautata rayuwar al’ummar Hungary.
A nasa bangare, shugaba Xi ya jaddada cewa, duk da cewa bai dade a Hungary ba, amma ya yi shawarwari masu zurfi, tare da cimma matsaya a fannoni da dama tare da shugabannin kasar. Xi na fatan kara yin mu’amala da firaminista Orban, da aiwatar da matsayar da suka cimma a zahirance, don samar da alfanu ga al’ummun kasashen biyu. (Murtala Zhang)