logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin: Kalaman Blinken sun jirkita gaskiya

2024-05-10 20:17:35 CMG Hausa

Rahotannin sun ruwaito cewa, sakataren harkokin wajen kasar Amurka, Antony Blinken ya bayyana a wajen wani dandalin tattaunawa da cibiyar nazari ta McCain ta shirya cewa, a harkokin kasuwancin kasa da kasa, kasar Sin ba ta da fifiko idan aka kwatanta da sauran wasu kasashe, akasin haka, tana nuna fifiko ne saboda rashin adalcin da take nuna wa sauran kasashe. Game da kalaman nasa, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau Jumma’a cewa, furucin Blinken ya sabawa manufofin tattalin arziki, kana ya jirkita hakikanin gaskiya.

Kakakin ya ce, a wani bangare, Amurka tana sukar kasar Sin, a dayan bangaren kuma, tana nuna fuskoki biyu, wato tana aiwatar da ma’aunai biyu, domin nuna fin karfi da babakere. Ya ce kasar Sin na bukatar Amurka ta mutunta manufofin tattalin arzikin kasuwanni, da bin ka’idojin tattalin arziki da kasuwancin kasa da kasa, da dakatar da shafawa kasar Sin bakin fenti tare da bata mata suna, da daina zargin sauran kasashe bisa fakewa da dalilin tsaron kasa. (Murtala Zhang)