logo

HAUSA

Isra’ila ta ci gaba da kaddamar da hare-hare a Rafah yayin da aka gaza cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

2024-05-10 10:30:26 CMG Hausa

 

Wani jami’i a gwamnatin Isra’ila ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, sojojin Isra’ila sun ci gaba da kaddamar da hare-hare ta kasa a birnin Rafah na kudancin zirin Gaza kamar yadda aka tsara, yayin da aka gaza cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas a tattaunawar jiya Alhamis a Alkahira da ke kasar Masar.

Jami’in da ba a bayyana sunansa ba, ya tabbatar da cewa, tawagar Isra’ila ta baro birnin Alkahira bayan tattaunawa da wakilan Hamas, inda masu shiga tsakani daga Amurka, da Masar, da Qatar suka yi yunkurin ganin an kawo karshen dauki ba dadi, da cimma nasarar sakin mutanen da ake tsare da su a Gaza.

To sai dai jami’in bai fayyace ko Isra’ila za ta fadada hare-haren da take kaddamarwa ba daga Rafah zuwa karin yankunan dake karshen kudancin Gaza, inda Falasdinawa ‘yan gudun hijira kimanin miliyan 1 da dubu dari 2 ke samun mafaka.

A daya bangaren kuma, wakilin Xinhua dake bibiyar halin da ake ciki game da rikicin, ya ce an girke dandazon sojojin Isra’ila a kan iyakar birnin Rafah.  (Saminu Alhassan)