logo

HAUSA

Firaministan Sin: A samar da karin alfanu da tsaro mai dorewa ga jama'a

2024-05-10 11:30:31 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi rangadi a jihar Xinjiang ta kasar Sin, tsakanin ranar 7 da ta 9 ga watan nan, inda ya jaddada cewa, kamata ya yi jihar ta yi amfani da albarkatunta wajen raya wasu sana'o'in da take da fifiko a cikin su, kana ta kara bude kofa ga sauran wuraren kasar, gami da kasashen waje, ta yadda za a iya tabbatar da ci gaban tattalin arziki mai inganci a jihar, don samar da karin alfanu, da tsaro mai dorewa ga al'ummar wurin.

A cewar Li Qiang, ana gina cibiyar zirin tattalin arziki na hanyar siliki a jihar Xinjiang, inda ya kamata a kara kokarin hada lardunan dake tsakiyar kasar Sin da kasashen dake dab da hanyar, don zurfafa hadin gwiwarsu a fannin tattalin arziki da cinikayya, da mai da jihar Xinjiang kofar kasa ga kasuwannin dake yammacin kasar Sin.

Har ila yau, Li ya jaddada bukatar daukaka matsayin layin jirgin kasa da ya hada kasar Sin da kasashen Turai, da raya sana'o'i daban daban a wuraren dake dab da layin, musamman ma gina wasu yankuna masu alaka da shige da fice, tare da samar da yanayi mai kyau ga aikin raya masana'antu.

Bayan da ya saurari labarin yadda yawan 'yan kasashen waje da suka ziyarci Xinjiang ya karu sosai, bayan ba da damar shiga jihar ba tare da bukatar neman izinin shiga kasa ba, Li Qiang ya ce, ya kamata a dora muhimmanci kan fannonin ciniki, da aikin ilimi, da aikin jinya, da al’adu, da yawon shakatawa, da dai sauran sana'o'i, don karfafa cudanya, da habaka mu'ammalar al'adu tsakanin al'ummun kasar Sin da na kasashen ketare. (Bello Wang)