Sin ta bayyana adawa da takunkuman Amurka kan kamfanoninta
2024-05-09 20:19:30 CMG Hausa
Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce kasar na matukar bayyana adawa da matakin da Amurka ta dauka, na kakaba takunkumai kan kamfanonin Sin guda 20, bisa zargin wai suna tallafawa sashen masana’antun kayayyakin soji, da na bunkasa makamashi na kasar Rasha.
Da yake bayyana rashin amincewar Sin da matakin na Amurka a Alhamis din nan, yayin taron manema labarai da ya gudana, mai magana da yawun ma’aikatar He Yadong, ya ce har kullum Sin na adawa da matakan kakaba takunkumai na kashin kai, wadanda ba su da tushe a dokokin cudanyar kasa da kasa, ba su kuma samu amincewar kwamitin tsaron MDD ba.
He Yadong ya kara da cewa, "A wani mataki na nuna fin karfi da danniya ta fuskar tattalin arziki", Amurka ta kakabawa wasu kamfanonin Sin takunkumai bisa zargin wai suna da alaka da Rasha, yayin da a hannu guda kuma Amurkar ke cewa tana da moriya a cinikayyar ta da Moscow.
Jami’in ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta gaggauta dakatar da aiwatar da matakan dakile kamfanonin kasar Sin, kuma Sin din za ta aiwatar da matakan da suka wajaba, na tabbatar da kare halastattun hakkoki da moriyar kamfanonin kasar Sin. (Saminu Alhassan)