logo

HAUSA

Peng Liyuan da Tamara Vucic sun ziyarci babban gidan adana kayan tarihi na Serbia

2024-05-09 04:22:20 CMG Hausa

Peng Liyuan, mai dakin shugaban kasar Sin Xi Jinping, ta ziyarci babban gidan adana kayan tarihi na kasar Serbia, tare da mai dakin shugaban kasar Serbia, Tamara Vucic a ranar Laraba.

Yayin da take zagayawa domin kallon zane-zanen dake cikin gidan na adana kayan tarihi, uwar gida Peng ta ce gidan na da dadadden tarihi da kayayyaki masu kima. Ta ce baya ga kasancewar gidan adana kayan tarihin wata kafa ta kiyayewa da baje kolin abubuwan al’adu, yana kuma kasancewa wani zaure na yayata wayewar kai. Kaza lika Peng ta yi fatan ganin an karfafa musayar al’adu, da hadin gwiwa tsakanin Sin da Serbia, tare da hada karfi wajen gina gadar tattaunawa dangane da wayewar kawuna.

An gina babban gidan adana kayayyakin tarihi na kasar Serbia tun a shekarar 1844, kuma yana kunshe da sama da kayan tarihi 400,000, adadin da ya sanya shi zama mafi girma da tsufa a kasar Serbia.(Saminu Alhassan)