logo

HAUSA

Shugaban Sudan ya ce babu wata tattaunawa ko tsagaita bude wuta har sai an fatattaki dakarun sa-kai

2024-05-09 17:15:27 CMG Hausa

A jiya Laraba ne shugaban majalisar rikon kwarya ta kasar Sudan Abdel Fattah Al-Burhan ya ce ba za a yi tattaunawa ko tsagaita bude wuta ba, har sai an fatattaki dakarun sa-kai na gaggawa na RSF.

Al-Burhan, wanda kuma shi ne babban kwamandan sojojin kasar Sudan (SAF), ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga rundunar sojojin kasar a jihar Kogin Nilu dake arewacin Sudan, a cewar majalisar wakilan kasar a cikin wata sanarwa.

Kalaman na Al-Burhan na zuwa ne kwana guda bayan wani kazamin fada tsakanin SAF da RSF a jihar Kordofan ta Arewa.

An dai gabatar da wasu tsare-tsare na zaman lafiya domin kawo karshen rikicin da ake fama da shi a kasar Sudan, ciki har daga kungiyar Tarayyar Afirka, da kungiyar raya kasashe masu tasowa, da kungiyar kasashen gabashin Afirka, da Saudiyya, da kuma Amurka, amma duk da haka sun ci tura.

Tun bayan barkewar rikici tsakanin SAF da RSF a ranar 15 ga Afrilun shekarar 2023, an samu rahoton mutuwar mutane kusan 15,000, yayin da adadin mutanen da suka rasa matsugunansu a ciki da wajen Sudan ya kai miliyan 8.2, a cewar alkalumman baya bayan nan da ofishin MDD mai gudanar da ayyukan Jin kai. (Mohammed Yahaya)