Amurka ta dakatar da samar wa Isra’ila taimakon kayayyakin soja
2024-05-09 15:40:32 CMG Hausa
Wani jami’in kasar Amurka ya bayyana jiya Laraba ranar 8 ga wata, cewar gwamnatin Amurka ta riga ta dakatar da samar wa kasar Isra’ila taimakon kayayyakin soja. Dalilin kuwa shi ne sabo da Amurka na damun yadda matakin soja da Isra’ila ke dauka a birnin Rafa dake kudancin zirin Gaza zai haddasa mutuwa da jikkatar dimbin fararen hula.
A ranar, ministan tsaron kasar Amurka Lloyd Austin ya bayyana cewa, ma’aikatarsa za ta ci gaba da tabbatar yadda Isra’ila ta samu makaman da take bukata don tsaron kanta, amma bisa halin da birnin Rafa ke ciki yanzu, ana sake bitar wasu tsoffin shirye-shiryen samar wa Isra’ila taimakon aikin soja. Austin ya yi wannan tsokaci ne yayin da yake ba da shaida a gaban majalisar dattawa ta Amurka don ma’aikatarsa ta samu kasafin kudi na shekarar 2025. (Kande Gao)