logo

HAUSA

CMG ya shirya harkar cudanyar al’adu a birnin Budapest don murnar cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Hungary

2024-05-09 09:51:24 CMG Hausa

A ranar 8 ga wata, babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG da asusun goyon bayan kafofin watsa labarai da kula da kadarorinsu na kasar Hungary na MTVA sun shirya harkar cudanyar al’adu a birnin Budapest don murnar cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Hungary, gami da kaddamar da aikin watsa shirin talibijin mai taken “Samun Dama A Sin” a kasar Hungary da kuma hadin gwiwar daukar wasu fina-finan gaskiya wato Documentary.

An yi harkar ce a daidai lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke ziyarar aiki a kasar Hungary, wadda ta samu halartar tsohon shugaban kasar Pál Schmitt, shugaban CMG Shen Haixiong, da babban daraktan MTVA Dániel Papp da dai sauransu.

A cikin jawabin da ya gabatar, Mr. Schmitt ya bayyana cewa, wannan harkar cudanyar al’adu ta kasance abin koyi ta fuskar hadin kan kafofin watsa labarai na kasashen biyu. Ana sa ran CMG zai taka rawar gani ga dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu, da kusantar da jama’ar kasashen biyu, a kokarin kara inganta dangantakar abokantaka a tsakanin Hungary da Sin daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare. (Kande Gao)