logo

HAUSA

Hadin Gwiwar Sin Da Turai Zai Yaukaka Daidaiton Dangantaka

2024-05-09 17:37:17 CMG Hausa

Ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke gudanarwa a kasashen Faransa, da Serbia, da Hungary, ta kasance muhimmin matakin yaukaka dangantakar diflomasiyyar bangarorin biyu.

Kasar Sin da kasashen Turai karkashin jagorancin kungiyar EU, muhimman bangarori ne biyu dake ingiza manufar samar da tasirin fada-a-ji daga bangarori daban daban, kuma sassan biyu na matukar goyon bayan dunkulewar duniya, a bangare daya kuma, sun kasance bangarori masu rungumar mabanbantan wayewar kai a duniya. Don hake ne ma masharhanta da dama ke kallon alakar Sin da Turai a matsayin mai da matukar muhimmanci wajen saita akalar ci gaban duniya baki daya.

Masu fashin baki na ganin cewa, Sin da kasashen tarayyar Turai ba su da manyan banbance-banbancen neman cimma moriya, ko sabani ta fuskar siyasar yankunan su. Kaza lika, batutuwan da suke dunkule sassan biyu wuri guda, sun rinjayi banbance-banbancensu. Hakan ne kuma ya sa har kullum suke ta kokarin yaukaka alakar su, ta yadda za su ci gaba da kasancewa sahihan kawaye abun koyi, su kuma ci gaba da yin hadin gwiwa, da cimma moriya tare a yanzu da ma nan gaba.

A bangarenta, a ko da yaushe kasar Sin na daukar tarayyar Turai a matsayin muhimmin karfi dake da tasiri a harkokin kasa da kasa, tana kuma sanya batun raya dangantakarta da EU a sahun gaba cikin harkokin diflomasiyyarta.

Bisa hakan ne ma a bazarar shekarar 2014, shugaba Xi ya ziyarci helkwatar kungiyar EU, inda a lokacin ya gabatar da shawarar hada karfi da karfe tsakanin kasarsa da EU, a fannonin wanzar da zaman lafiya, da samar da ci gaba, da gudanar da sauye-sauye, da bunkasa wayewar kai. Har yanzu kuma wannan kuduri bai sauya ba, yana kuma ci gaba da zama alkiblar raya dangantakar sassan biyu a halin da ake ciki yanzu.

Yayin da duniya ke kara tsunduma cikin hali na rashin tabbas, da rigingimu nan da can, yana da kyau Sin da EU su wanzar da tattaunawa ta kut da kut, su kuma mayar da hankali ga hadin gwiwar cimma moriyar juna, daga fannin ingiza ci gaban bangarorin biyu zuwa tunkarar kalubalolin dake addabar duniya baki daya.

Tabbatattun shaidu sun nuna cewa, muddin Sin da EU sun yi aiki tare wajen saita alkiblar da za su bi domin bunkasa kan su, ko shakka babu hakan zai iya kai su ga cimma burikan da suka sanya gaba, tare da haifarwa al’ummun su da tarin alherai.

A halin da ake ciki, Sin na kan gaba a jerin sassa mafiya muhimmanci ga Turai a fannin hada-hadar cinikayya. Duk da tafiyar hawainiya da tattalin arzikin duniya ke yi a yanzu, a shekarar bara, jimillar darajar cinikayya tsakanin Sin da EU ta kai dala biliyan 783. Kaza lika Sin na yiwa Turai maraba a fannonin cin gajiyar hadin gwiwar kasuwanci, da raya kimiyya da fasaha, da bunkasa hidimomin sarrafa hajojin masana’antu da rarraba su ga sassan duniya, ta yadda sassan biyu za su ci gajiyar bai daya, da samun nasara da walwala tare.

Ko shakka babu sannu a hankali, hadin gwiwar Sin da Turai na bunkasa, musamman ma a fannonin da duniya ke mayar da hankali yanzu a kansu, kamar tattalin arziki na dijital, da bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da cin gajiya daga sabbin makamashi, da kirkirarriyar basira.

Bunkasar Sin wata dama ce ga EU, kana daidaita kawancen sassan biyu zai taimaka matuka wajen shawo kan kalubale da EU ke fuskanta. A halin da ake ciki, karin sassan Turai na dada fahimtar muhimmancin hada gwiwa da Sin, wajen magance matsalolin makamashi, da hauhawar farashin hajoji da EU ke fuskanta, a daya bangaren dangantakar sassan biyu za ta kyautata takara mai tsafta tsakaninsu, da haifar da gajiya ga Sin da turai da ma duniya baki daya. (Saminu Alhassan)