Sin: Haramta Fitar Da Kwakwalwar Kwamfuta Ga Huawei Da Amurka Ta Yi “Barazana Ce Ga Kasuwanci”
2024-05-09 10:51:45 CMG Hausa
Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin a ranar Laraba ta zargi Amurka da yin “Barazana ga Kasuwanci” kan soke lasisin da ta baiwa kamfanoni damar fitar da kwakwalen kwamfuta wato Chips ga Huawei, babban kamfanin fasaha ta kasar Sin.
Kakakin ma’aikatar a cikin martaninsa ga binciken kafofin yada labarai kan soke lasisin ya ce, kasar Amurka ta mai da manufar tsaron kasa ta zama ta gama-gari, da kuma siyasantar da batutuwan tattalin arziki, da kin mutunta matakan fitar da kayayyaki zuwa waje, da kuma ci gaba da daukar matakai mara ma’ana don dakile kamfanonin Sin.
Kakakin ya ce, takunkumin da Amurka ta kakaba kan fitar da kwakwalwar kwamfuta na farar hula zalla zuwa kasar Sin, da kuma aiwatar da kayyade wa wani kamfani na kasar Sin samun kayayyaki, ya kasance barazana ga kasuwanci karara.
Wannan tsari ba wai kawai ya saba wa ka'idojin kungiyar cinikayya ta duniya ba, har ma yana cutar da muradun kamfanonin Amurka sosai.
Kakakin ya kara da cewa, kasar Sin za ta dauki dukkan matakan da suka dace don kiyaye hakki da moriyar kamfanonin kasar Sin. (Yahaya)