logo

HAUSA

A kalla mutane 30 ne suka mutu yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare ta kasa a yankin Rafah na Gaza

2024-05-09 10:22:28 CMG Hausa

 

Rundunar sojojin Isra’ila ta sanar a ranar Laraba cewa, tana ci gaba da kai hare-hare ta kasa a yankin Rafah na Gaza, inda ta bayar da rahoton mutuwar mutane kusan 30 tun bayan fara kai farmaki a daren Litinin.

A cewar sanarwar da sojojin suka fitar. Mutane 30 din da suka mutu mayaka ne, yayin da jami’an kiwon lafiya na Gaza suka bayar da rahoton mutuwar kimanin mutane 35, ciki har da wani jariri dan wata hudu.

Rundunar sojin ta ce, wani bangare na sojojin masu amfani da tankokin yaki da kuma masu sulke na aiki a kasa a gabashin Rafah, yayin da jiragen yaki marasa matuka suka kai hare-hare ta sama.

Sun kai hari kan kusan “wurare 100” a yankin, da suka hada da ababen more rayuwa na ’yan bindiga da “gine-gine masu shakku” inda mayakan Hamas suka yi harbi kan sojojin Isra’ila, a cewar rundunar.

Isra'ila ta kai farmaki ta kasa a Rafah a cikin dare tsakanin Litinin da Talata, bisa manufarta na kawar da bataliyoyin Hamas hudu da suka rage a kudancin birnin.

Dakarun sun yi “nasarar karbe” yankin daga hannun mayakan Gaza na mashigar Rafah a ranar Talata, wata muhimmiyar hanyar shigar da agajin jin kai daga Masar zuwa cikin Gaza da ke fama da yunwa, tare da rufe shi. (Yahaya)