logo

HAUSA

Hukumar raya yankunan arewa maso gabashin Najeriya ta fara horas da matasa kan fasahar saka na’urorin wutar hasken rana

2024-05-09 09:07:25 CMG Hausa

 

Hukumar raya yankunan arewa maso gabashin Najeriya ta fara gudanar da shirin bayar da horo na tsawon makonnin 6 ga wasu matasan yankin su 30  kan fasahar saka na’urar samar da wutar hasken rana.

A lokacin da yake kaddamar da shirin bayar da horon a garin Gombe a farkon wannan mako, mukaddashin ko-odinetan hukumar a jihar Alhaji Rufa’i Baba-Manu ya ce, yayin horon, matasan za su samu kwarewa a fannonin hada solar da kuma kasuwancin ta.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwia ya aiko mana da rahoto. 

Alhaji Rufa’i Baba-Manu ya ce, bayan kammala bayar da horon ana sa ran cewa matasan za su kasance masu dogaro da kansu ta fuskar aikin yi, sannan kuma sana’ar tasu za ta yi sanadin kawo karshen matsaloli na karancin wuta da ake fuskanta a shiyyar baki daya.

A nasa jawabin, manajan daraktan hukumar ta raya yankunan arewa maso gabashin Najeriya Alhaji Mohammad Alkali wanda kuma ya samu wakilcin manajan sashen ayyukan jin kai, jaddada kudurin hukumar ya yi na ci gaba da kirkiro shirye-shiryen da za su kyautata yanayin rayuwa da na tattalin arzikin al’ummar shiyyar.

Shi ma da yake nasa jawabi, kwamishinan kimiya da fasaha na jihar Gombe Alhaji Abdullahi Ahmed yabawa hukumar ya yi bisa hangen nesanta wajen kirkiro da wannan shirin na bayar da horo.

Ya ce da jimawa daman ya kamata arewacin Najeriya a koma amfani da na’urar wutar solar.

“Yanzu abun da muke bukata shi ne yadda za a rinka gyaran solar, wato dai idan mun koma kachakon kan amfani da wannan sabon makamashi na solar ta kuma wace hanya za mu rinka gyara ta, a sabo da haka wannan horo ya zo a lokacin da ya kamata. (Garba Abdullahi Bagwai)