Shugabannin kasashen Sin da Serbia sun gana da manema labaru
2024-05-08 18:45:47 CMG Hausa
Yau Laraba 8 ga wata a birnin Belgrade, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Serbia sun gana da manema labaru, bayan kammala shawarwari.
Xi Jinping ya bayyana cewa, idan aka waiwayi tarihi, abotar Sin da Serbia ta samu ne ta hanyar gwagwarmayar hada hannu domin neman tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya, wadda jini da rai suka karfafa ta. Gina al’umma mai makoma ta bai daya ga Sin da Serbia a sabon zamani, wani muhimmin zabi ne da kasashen biyu suka yi. Manufar hakan ita ce cimma burikan al’ummomin biyu na samun kyautatuwar rayuwa. Haka kuma, goyon baya da gudunmuwar al’ummomin biyu su ne ginshiki da karfin dake ingiza dangantakarsu. Ya ce, a shirye Sin take ta hada hannu da Serbia wajen kama sabon tafarkin gina al’umma mai makoma ta bai daya ga Sin da Serbia a sabon zamani, tare da ci gaba da kara bunkasa dangantakar. (Bilkisu Xin & Fa’iza Mustapha)