logo

HAUSA

Xi ya wallafa makalar da ya sanya hannu a jaridar Hungary

2024-05-08 14:11:47 CMG Hausa

Yau Laraba 8 ga wata, kafin ziyarar aikinsa a kasar Hungary, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya wallafa makala mai taken “Hada kai domin ciyar da huldar dake tsakanin kasar Sin da kasar Hungary gaba yadda ya kamata” da ya sanya hannu a jaridar Magyar Nemzet ta Hungary.

A cikin makalarsa, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, bana ce ta cika shekaru 75 da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Hungary. A cikin wadannan shekaru 75, al’ummun kasashen biyu suna sada zumunta mai zurfi tsakaninsu, kuma sassan biyu suna biyayya ga juna domin samun ci gaba tare.

Xi ya kara da cewa, “A halin yanzu, kasar Sin da kasar Hungary suna cikin zamani mai muhimmanci yayin da suke kokarin raya kasa. Ina fatan ziyarata za ta kara zurfafa dadadden zumuncin dake tsakaninmu, kuma za ta kara karfafa hadin gwiwar sassan biyu, ta yadda za a ciyar da huldar abota tsakanin Sin da Hungary gaba zuwa wani sabon mataki.”

A cewarsa, ya dace kasashen biyu su kara karfafa cudanya da hadin gwiwa domin samun ci gaba mai inganci tare, kuma su kara karfafa musayar al’adu da harkokin kasa da kasa, da hadin gwiwar shiyya shiyya, ta yadda za su dakile kalubalen dake gaban daukacin kasashen duniya, tare kuma da kiyaye zaman lafiya da ingiza bunkasuwa a fadin duniya. (Jamila)