Tiktok ta kai gwamnatin Amurka kotu don hana haramta ta
2024-05-08 11:18:21 CMG Hausa
A jiya Talata ne Tiktok, dandalin nishadi na bidiyo ta yanar gizo, da mamallakinta mai suna ByteDance, wani kamfanin kasar Sin, suka shigar da karar gwamnatin Amurka gaban kotu kan wata doka da ta tilasta wa ByteDance sayar da shahararriyar manhanjarta ko a haramta amfani da ita a kasar. Shugaban Amurka Joe Biden ya sanya hannu kan dokar haramta Tiktok a watan da ya gabata bayan majalisun dokokin kasar sun amince da ita.
TikTok a cikin karar da aka shigar a kotun daukaka kara na gundumar Columbia ya ce, "A karon farko a tarihi, Majalisa ta kafa wata doka wacce ke ba damar hana amfani da dandalin sada zumunta guda daya tak zuwa haramtawa ta dindindin a kasa baki daya, da kuma hana kowane Ba'amurke yin mu’amala cikin wata al'umma ta musamman ta yanar gizo tare da mutane sama da biliyan 1 a duk duniya."
TikTok ya ce, "Haramta amfani da TikTok rashin bin tsarin mulki ne a bayyane, hakika, har masu tallafawa dokar sun fahimci gaskiyar hakan, don haka sun yi matukar kokarin nuna cewa dokar ba ta matsayin haramci kwata-kwata, sai dai kawai ka'ida ce ta mallakar TikTok," a cewar TikTok. (Mohammed Yahaya)