Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Serbia Vučić
2024-05-08 18:08:10 CMG Hausa
Da safiyar yau Laraba, 8 ga wata bisa agogon wurin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Serbia Aleksandar Vučić a Belgrade, inda shugabannin biyu suka sanar da zurfafawa da karfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakaninsu, da kuma bude wani sabon babi na kafa kyakkyawar dangantaka a tsakaninsu.
A wani sabon mafarin tarihi, kasar Sin tana son yin aiki tare da kasar Serbia don ci gaba da karfafa dangantakar abokantaka, da riko da raya dangantakar dake tsakaninsu, tare da kiyaye muhimman muradun kasashen biyu masu dorewa, da neman ci gaban kasashensu da farfado da al’ummunsu kafada da kafada, kana da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga kasashen biyu a sabon zamani, ta yadda za su bada gudummowa ga inganta gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga bil’adama. (Bilkisu Xin)