logo

HAUSA

Sahihanci Ya Sa Kasar Sin Samun Karbuwa A Nahiyar Afirka

2024-05-08 19:48:31 CMG Hausa

Shahararren kamfanin tantance ra'ayin jama'a na Gallup, ya gabatar da wani sakamakon binciken da ya yi a kwanan baya, inda ya ce kasar Sin ta zarce kasar Amurka, ta zama wadda ta fi tasiri a nahiyar Afirka. Alkaluman da kamfanin ya gabatar sun nuna cewa, 'yan Afirka da suke goyon bayan kasar Sin, sun karu daga kashi 52% a shekarar 2022, zuwa kashi 58% a shekarar 2023. Yayin da a daya bangaren, masu goyon bayan kasar Amurka suka ragu daga kashi 59% a shekarar 2022, zuwa kashi 56% a bara.

Wannan sakamakon bincike ya yi daidai da sakamakon nazari da wasu hukumomin binciken ra'ayin jama'a na kasashen Afirka, irinsu Afrobarometer mai hedkwata a kasar Ghana, da Ichikowitz Family Foundation dake kasar Afirka ta Kudu, suka gabatar, inda dukkansu suka sanya kasar Sin a gaban kasar Amurka, a fannin samun karbuwa.

Sai dai me ya sa masu goyon bayan kasar Amurka suka ragu? Kamfanin Gallup bai yi wani karin bayani ba. Amma a ganina a kalla akwai dalilai 2.

Na farko, kasar ta kan keta adalci a al'amuran duniya. Misali, a rikicin Falasdinu da Isra'aila na wannan karo, kasar Amurka ta yi ta samar da tallafin makamai ga Isra'ila, abin da ya haddasa dorewar rikicin, gami da tsanantar matsalar jin kai, lamarin da ya janyo dimbin suka daga gamayyar kasa da kasa.

Na biyu, yadda kasar ke kallon kanta kamar "baba", da son tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe. Misali, a nahiyar Afirka, kasar Amurka ta nemi hana kasar Uganda zartas da dokar haramta luwadi, da hana kasar Niger kulla hulda da Rasha da Iran, da dai sauransu.

Sa'an nan a daya bangaren, dalilin da ya sa kasar Sin kara samun karbuwa a nahiyar Afirka, shi ne yadda ta magance kurakuran da Amurka ta tabka. A cewar wani shehun malami mai suna Adhere Cavince na kasar Kenya, manufar diplomasiyya ta kasar Sin ta jaddada muhimmancin girmama ikon mulkin kai na sauran kasashe, da rashin tsoma baki cikin harkokin gidansu, da kallon kanta a matsayin kawa maimakon babbar kasar dake da karfi. Wadannan manufofi na kasar Sin sun burge kasashen Afirka, wadanda suka dade suna shan wahalar mulkin mallaka, da shisshigin da kasashen yamma suke yi musu.

Cikin wani bayani mai taken " Me ya sa kasar Sin ta fi kasar Amurka samun karbuwa a nahiyar Afirka?" da Mista Cavince ya rubuta, wanda aka buga cikin jaridar the Nation ta kasar Kenya, ya ce, kasar Sin na dora muhimmanci kan hadin gwiwa a bangaren tattalin arziki, ba tare da gindaya sharadi na siyasa ba, sabanin abun da kasar Amurka ta kan yi, na alakanta tallafi da zuba jari da sharuda na siyasa, irinsu batun hakkin dan Adam, da tsarin da ake bi wajen gudanar da mulki. Ta wannan hanya, kasar Sin ta samar da dimbin damammaki ga kasashen Afirka, na kiyaye tsarinsu na siyasa, gami da neman dabarar raya tattalin arziki, a lokaci guda.

Ban da haka, Mista Cavince ya ambaci hakikanin ci gaban da kasar Sin ta haifar wa nahiyar Afirka. Inda hadin gwiwar "Ziri Daya da Hanya Daya" ya inganta kayayyakin more rayuwa na kasashen Afirka, da ba da damar raya tattalin arziki, da dunkulewar kasashen Afirka waje guda. Kana zuba jari da kasar Sin take yi ya zama muhimmiyar damar samun kudin shiga da guraben aikin yi ga kasashen Afirka. Haka zalika, yadda kasar Sin ke samar da kudin tallafin karatu ga daliban Afirka domin su yi karatu a kasar Sin, ya karfafa cudanya tsakanin al'ummun bangarorin 2, da ba matasan kasashen Afirka damar kara fahimtar kasar Sin. Sa'an nan ta hanyar raba nagartattun fasahohinta, kasar Sin ta zame wa kasashen Afirka muhimmiyar kawar hadin kai, a kokarinsu na neman ci gaban kasa.

Hakika ainihin dalilin da ya sanya kasar Sin daukar wadannan matakai shi ne tunanin kasar na musamman a fannin hadin gwiwa da kasashen Afirka, wato gaskiya, da kauna, da sahihanci, gami da samar da hakikanin sakamako. Idan wata kasa, yayin da take hulda da sauran kasashe, ta iya nuna wani yanayi na daidaito, da rashin yaudara ta akidar siyasa, da kokarin cika alkawarin da ta dauka, da samar da hakikanin alfanu ga sauran kasashe, ta hanyar hadin gwiwar ta moriyar juna, to, ba za a ki kaunarta ba. Saboda haka, za mu iya cewa, wannan ra'ayi na nuna sahihanci, da samar da hakikanin sakamako na kasar Sin, shi ne tushen hulda mai kyau dake tsakaninta da kasashen Afirka.

Bisa haka, za mu iya hasashen cewa, bayan kasar Sin da kasashen Afirka sun kara karfafa hadin kansu na amfanawa juna a kai a kai, huldar dake tsakaninsu ma za ta kara kyautatuwa. (Bello Wang)