logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a samar da sharadi ga gudanarwar siyasa a Abyei

2024-05-08 10:46:39 CMG Hausa

A jiya 7 ga wannan wata ne mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Dai Bing ya yi kira a gun taron da kwamitin sulhun majalisar ya kira domin tattauna yanayin siyasa da Abyei ke ciki, da a samar da sharadi ga sake gudanar da harkokin siyasa a yankin.

Dai Bing ya bayyana cewa, ana gwabza rikici a kasar Sudan, wanda ya kawo illa ga yanayin Abyei, ‘yan gudun hijira da yawan gaske sun shiga yankin, lamarin da ya tsananta yanayin jin kai da karancin albarkatu, har ya kawo cikas ga gudanarwar siyasa a yankin. Don haka kasar Sin tana fatan kasar Sudan ta kawo karshen hargitsin tun da wuri wuri, kuma ta maido da tattaunawa da hadin gwiwa dake tsakaninta da kasar Sudan ta Kudu, saboda hakan zai taimaka wajen sake gudanar da harkokin siyasa a yankin Abyei.

Jami’in ya kara da cewa, har yanzu hargitsin dake tsakanin kabilu yana ci gaba da kasancewa muhimmiyar matsalar da yankin ke fuskanta a bangaren tsaro. Kasar Sin tana goyon bayan kokarin da rundunar sojojin wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Abyei ke yi domin daidaita sabani dake tsakanin kabilu daban daban a yankin ta hanyar tattaunawa, ta yadda za a cimma burin shimfida zaman lafiya a yankin. Kasar Sin a shirye take ta ci gaba da kokartawa tare da sauran kasashen duniya domin ba da karin gudummowa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin na Abyei. (Jamila)