logo

HAUSA

Jawabin shugaba Xi Jinping a filin jirgin sama na Kasar Serbia

2024-05-08 04:51:08 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping dake ziyarar aiki a Serbia, ya gabatar da jawabi bayan saukarsa a filin jirgin sama na Nikola Tesla dake Belgrade na kasar, A ranar 7 ga Wata.

Cikin jawabin, Xi Jinping ya ce Sin da Serbia, suna more dadaddiyar abota mai zurfi. Kuma dangantakar dake tsakaninsu ta jure duk wani sauyi da yanayin duniya ya kawo, tare da zama kyakkyawar abar misali a dangantakar kasa da kasa. Ya ce a shirye kasar Sin take ta hada hannu da Serbia wajen nacewa ga ainihin burinsu da samun ci gaba tare domin bude wani sabon babi na dangantakarsu, mai karin kuzari da fadi da kuma matukar inganci. (Fa’iza Mustapha)