Shugabannin Sin da Faransa sun gana a Hautes-Pyrenees
2024-05-08 04:18:41 CMG Hausa
A ranar 7 ga wata, bisa agogon kasar Faransa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci lardin Hautes-Pyrenees na kasar, bisa gayyatar da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi masa.
Emmanuel Macron da mai dakinsa Brigitte Macron sun jira shugaba Xi da uwargidansa Peng Liyuan, a wani wurin hutu na makiyaya dake bakin tsaunin Col du Tourmalet, inda suka kalli wata rawa ta musamman da aka taka, gami da daukar hoto tare.
Yayin hirarsu, shugaba Xi Jinping ya ce, kasashen Sin da Faransa suna da mabambantan al'adu, amma dukkansu na son yin cudanya da koyi da juna. Saboda haka ya kamata su yi musaya da hadin gwiwa, don samar da gudunmowa ga kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya. A nasa bangare, shugaba Macron na Faransa ya ce, yana son karfafa mu'ammala tsakaninsa da shugaba Xi Jinping don taimakawa wajen kare zaman lafiya a nahiyar Turai, da ma duniya baki daya. (Bello Wang)