logo

HAUSA

Matsayar Sin da Faransa ta bayyana lamirin bil Adama na kare adalci

2024-05-08 11:04:46 CMG Hausa

Yayin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai kasar Faransa a ranar 6 ga wannan wata, kasashen biyu sun fitar da “Hadaddiyar sanarwar kasashen Sin da Faransa kan yanayin siyasa da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki”, inda sassan biyu suka cimma matsaya guda daya kan batutuwa da dama da suka kunshi rikicin Palastinu da Isra’ila, da batun nukiliya na Iran, da rikicin Bahar Maliya da sauransu, kuma suka bayyana ra’ayinsu tare. Sanarwar da suka fitar a daidai lokaci ta hada da bayanai da dama, wadanda suka bayyana lamirin bil Adama na kare adalci, kuma ta nunawa al’ummun kasa da kasa cewa kasashen Sin da Faransa suna sauke nauyin da ke bisa wuyansu wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya.

Yayin ziyararsa a Faransa, sau da dama shugaba Xi ya yi tsokaci kan batun Palastinu da Isra’ila, inda ya jaddada cewa, har yanzu ba a daidaita masifar ba, ana iya cewa, ya kasance jarrabawa ga lamirin bil Adama, dole ne kasashen duniya su dauki mataki domin dakile masifar. Xi ya yi nuni da cewa, yanzu abu mafi muhimmanci shi ne a tsagaita bude wuta daga duk fannoni, kuma a tabbatar da shirin “kafa kasashe biyu”. Bangaren Faransa shi ma ya nuna cewa, yana fatan zai yi hadin gwiwa da bangaren Sin domin kiyaye ra’ayin gudanar da harkokin kasa da kasa bisa bangarori daban daban, da ka’idojin MDD, da kuma dokokin kasa da kasa.

Hadaddiyar sanarwar da sassan biyu suka fitar ta bayyana duk wadannan ra’ayoyi, ko shakka babu, za ta taka babbar rawa kan hana tsananta yanayin siyasa da ingiza gudanar da shimfida zaman lafiya tsakanin Palastinu da Isra’ila. (Jamila)