logo

HAUSA

Tarayyar Afirka ta kaddamar da dabarun yaki da kwararowar hamada

2024-05-08 11:14:40 CMG Hausa

A jiya Talata ne kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta kaddamar da shirin yaki da kwararowar hamada a nahiyar na tsawon shekaru goma masu zuwa. Josefa Leonel Correia Sacko, kwamishiniyar aikin gona, raya karkara, tattalin arzikin teku da muhalli mai dorewa a hukumar tarayyar Afirka, ta bayyana hakan a birnin Nairobi, babban birnin Kenya, cewa sabuwar dabarar AU na shirin babban koren ganuwa ko the Great Green Wall Initiative a Turance, ta samar da tsarin daidaitawa da gudanar da matakai daban-daban, tare da ayyukan gama gari don maido da shimfidar wurare da gina al'ummomi masu juriya a busasshiyar kasa ta Afirka.

"Dabarun na binciko sabbin hanyoyin samar da kudade da karfafa gwiwa ta hanyar farfado da tsarin ayyukan kasa da za su ba da gudummawar ga hana kwararowar hamada," a cewar Sacko a yayin taron koli na biyu na fannin samar da taki da lafiyar kasa na Afirka da kungiyar AU ta shirya.

Taron na kwanaki uku ya tattara mahalarta sama da 4,000 na Afirka, da masana kimiyya da masu ba da taimako na kasa da kasa, don samar da muhimmiyar tattaunawa kan inganta kasa a nahiyar. (Mohammed Yahaya)