logo

HAUSA

Chang-e 6 ya shiga zagayen duniyar wata bayan birki kusa da wata

2024-05-08 16:27:18 CMG Hausa

Hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin (CNSA) ta sanar a yau Laraba cewa, na’urar Chang’e-6 mai binciken duniyar wata ta kasar Sin ta yi nasarar shiga falakin wata. 

Da karfe 10:12 na safiyar Laraba, agogon Beijing, Chang'e-6 ya yi nasarar yin birki a kusa da duniyar wata kafin ya shiga kewaye falakin wata, a cewar hukumar ta CNSA.

Tare da taimakon tauraron dan Adam na Queqiao-2, daga baya Chang'e-6 zai daidaita tsayuwa da kuma daukar saiti don kewayar duniyar wata, da zabar lokacin da ya dace don aiwatar da rabuwa tsakanin na’urar dawowa daga kewaye falakin wata da na’urar sauka da tashi a kan duniyar wata.

Daga bisani na’urar sauka da tashi za ta sauka a kan yankin kudancin duniyar wata da ake kira “South Pole-Aitken Basin” don aiwatar da aikin tattara samfura da dawowa daga gefen duniyar wata mai nisan gaske kamar yadda aka tsara. (Mohammed Yahaya)