logo

HAUSA

An bude wani dandalin kasuwanci tsakanin Nijar da Tunisia a birnin Yamai

2024-05-08 10:29:48 CMG Hausa

Goman shugabannin kamfanonin kasar Tunisia na ziyarar aiki a birnin Yamai, cikin tsarin dandalin kasuwanci tsakanin kasashen biyu. Ministan kasuwanci da masana’antun kasar Nijar, Seydou Asman ya kaddamar daga ranar 6 har zuwa 8 ga watan Mayun shekarar 2024.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Shi dai wannan dandali mai cike da fa’ida ga ’yan kasuwan kasashen biyu, na da burin shimfida wata kyakkyawar tattaunawa kan musanya da zuba jari tsakanin ’yan kasuwar Tunisia da masu ruwa da tsaki kan harkokin tattalin arziki na Nijar.

Wannan dandalin tattalin arziki da kasuwanci da ya tara ’yan kasuwa maza da mata na kasashen biyu da zai kasance wani tsarin samar da damammakin zuba jari musamman ma a kasar Nijar.

Musanyar kasuwanci tsakanin Nijar da Tunisia ta tashi zuwa fiye da dalar Amurka miliyan 10 na shigo da kayayyaki daga kasar Tunisia, yayin da ya kai dalar Amurka dubu 31 na fitar da kayayyaki daga kasar Nijar a shekarar 2022. Haka zai iyar karuwa sosai a nan gaba ta yadda kowa zai ci gajiya tsakanin kasashen biyu tare da maida hankali wajen bunkasa bangaren masu zaman kansu.

A cewar ministan kasuwancin Nijar, Seydou Asman, bangaren masu zaman kansu ko shakka babu zai taimaka wajen kafa ayyukan yi ga matasanmu, da kuma samar da karin albarkatu domin bunkasa gine-ginen jin dadin al’umomi a fannin tattalin arziki, kiwon lafiya, makamashi, ruwa, otel, ilimi da kuma samar da dama a fannin kimiyya da fasaha da sadarwa.

Haka kuma ministan ya gayyaci mahalarta taron da su yi musanya bisa tunanin moriyar juna da kuma karfafa zumunci da ke tsakanin  kasashen Nijar da Tunusia, in ji minista Seydou Asman. (Mamane Ada)