Xi ya yi tsokaci kan hargitsin Palastinu da Isra’ila da rikicin Ukraine
2024-05-07 02:44:22 CGTN
Da yammacin ranar 6 ga wannan wata, agogon Faransa, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron sun yi ganawa da menama labarai bayan kammala tattaunawarsu, inda Xi ya bayyana matsayin kasar Sin kan hargitsin dake tsakanin Palastinu da Isra’ila da kuma rikicin Ukraine.
Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, yanzu duniyarmu tana fuskantar targarda, kasar Sin a shirye take ta gabatar da shawarar tsagaita bude wuta tare da bangaren Faransa a yayin gasar wasannin Olympics da za a gudana a birnin Paris, fadar mulkin kasar Faransa.
Game da hargitsin Palastinu da Isra’ila, Xi ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan a tsagaita bude wuta a zirin Gaza, kuma tana goyon bayan Palastinu da ta shiga MDD. Kana tana fatan za a maido da hakkin al’ummar Palastinu, da sake aiwatar da “shirin kafa kasashe biyu”, ta yadda za a tabbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.
Game da rikicin Ukraine, Xi ya jaddada cewa, duk da cewa kasar Sin kasa ce da ba ta tayar da rikici, amma ta dade tana yin kokari domin shimfida zaman lafiya. A sa’i daya kuma, kasar Sin tana adawa da duk wanda ke shafawa saura bakin fenti bisa fakewa da rikicin. Kuma ta yi kira ga bangarori daban daban da su sake yin tattaunawa domin kara fahimtar juna. Haka kuma tana fatan za a kira taron tattaunawa kan zaman lafiya tsakanin kasa da kasa da zai samu amincewa daga bangarorin Rasha da Ukraine. Hakazalika, kasar Sin tana goyon bayan a kafa tsarin tsaron nahiyar Turai mai dorewa.
Ban da haka, Xi ya yi tsokaci kan huldar dake tsakanin kasarsa da kasar Faransa, inda ya yi nuni da cewa, ya dace sassan biyu su yi kokari domin kara karfafa huldarsu bisa manyan tsare-tsare, da kara karfafa hadin gwiwa dake tsakaninsu, da kara hanzartar cudanyar al’adu da juna, da kuma kara habaka hadin gwiwa tsakanin dukkan kasashen duniya. (Jamila)