logo

HAUSA

Kamfanin gine-gine na kasar Sin CCG zai gudanar da aikin gina gadoji a unguwar Dan Agundi a cikin birnin

2024-05-07 09:31:51 CMG Hausa

 

A kokarin da take yi wajen mayar da birnin Kano kasaitacce tare da rage cunkoson ababen hawa, gwamnatin jihar Kano ta sake kaddamar da tagwayen gadoji a kofar Dan Agundi dake yankin karamar hukumar Birnin.

A lokacin da yake aza harsashin fara aikin gadojojin a ranar Lahadi da ta gabata, gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce, aikin zai ci tsabar kudi har Naira biliyan 15 wanda kamfanin gine-gine na kasar Sin CCG zai gudanar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.  

Gwamnan na jihar ta Kano ya ce, tun a watan Disambar bara na 2023, gwamnati ta bayar da kwangilar ga kamfanin na CCG bisa yarjejeniyar zai kammala aikin cikin watanni 18.

Ya ce, hakika aikin yana da muhimmancin gaske ga walwalar al’umma musamman masu ababen hawa, a sabo da haka ya bukaci al’umomin da suke zaune a yankunan da za a gudanar da wannan aiki da su baiwa kamfanin da zai gudanar da aikin cikakken hadin kan da ya kamata.

A jawabinsa yayin bikin kaddamar da fara aikin, manajan ayyuka na kamfanin CCG Mr. Gee Wang ya ce, yana da yakinin kamfanin zai cimma wa’adin da aka dibar masa wajen kammala aikin.

“Za mu yi bakin kokarinmu wajen tabbatar da ganin mun kammala aikin a iya tsawon watanni 18 da aka dibar mana, ba za mu yi baiwa gwamnati da al’ummar jihar Kano kunya ba wajen yin aiki mai inganci da na baya za su ci gajiya.” (Garba Abdullahi Bagwai)