Annobar cutar kyanda ta yi sanadin mutuwar yara 42 a jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya
2024-05-07 09:27:15 CMG Hausa
Gwamnatin jihar Adamawa ta sanar da bullar cutar kyanda a wasu kananan hukumomin jihar, wanda har ta yi sanadin mutuwar yara 42.
Kwamishinan lafiya na jihar Mr Felix Tangwami ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a birnin Yola, fadar gwamnatin jihar jim kadan da kammala taron majalissar zartarwar jihar a jiya Litinin 6 ga wata.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Kwamishinan lafiyar ya ce, ya baiwa majalissar zartarwar cikakken rahoto a game da barkewar wannan annoba a yankunan kananan hukumomi 18 in ban da karamar hukumar Lamurde.
Amma ya ce, tun daga ranar Asabar da ta gabata lokacin samun rahoton bullar annobar, gwamnatin ta tura jami’an kiwon lafiya da magunguna domin kai dauki yankunan da al’amarin ya faru.
“A yankin Mudi ta arewa mazabu 8 ne annobar ta bullar, yayin da kuma a Gombi mazabu 7, a yankin Mudi ta arewa an samu rahoton mutane 131 da ake zargin sun kamu da cutar a yankin karamar hukumar Gombi kuma 177, haka kuma mutane 23 ne suka mutu a yankin na Mubi ta arewa a yankin Gombi kuma 19.”
Kwamishinan ya tabbatar da cewa, saboda yaduwar cutar cikin gaggawa zuwa sauran kananan hukumomi 18, yanzu haka a samar da karin jami’an kiwon lafiya tare da wadatattun alluran riga kafin cutar.
Tun dai a jiya Litinin ma’aikatar ilimin jihar ta sanar da rufe dukkannin makarantun gwamnati da na masu zaman kansu dake jihar a wani matakin gaggawa na dakile yaduwar cutar. (Garba Abdullahi Bagwai)