Sassa daban daban na Serbia na dakon ziyarar shugaba Xi Jinping
2024-05-07 19:08:22 CMG Hausa
A kan titunan Belgrade, babban birnin kasar Serbia, ana iya ganin tutocin kasashen Sin da Serbia a ko ina, al'umma daga sassa daban-daban na kasar na dakon ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping.
Bisa gayyatar da takwaransa na Jamhuriyar Serbia Aleksandar Vučić ya yi masa, shugaba Xi Jinping zai gudanar da ziyarar aiki a kasar. Wannan ne karo na biyu da shugaba Xi ya kai ziyara kasar Serbia bayan shekaru 8. (Bilkisu Xin)