Sinawa ba za su manta da danyen laifin NATO na kai wa Yugoslavia hari ba
2024-05-07 19:43:03 CMG Hausa
Yayin taron ganawa da manema labaran da aka yi yau, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya mayar da martani game da batun harin da kungiyar NATO ta kai wa Yugoslavia, inda ya bayyana cewa, al’ummun Sinawa ba za su manta da wannan danyen laifin da NATO ta aikata ba.
Lin Jian ya yi nuni da cewa, “Kafin shekaru 25 da suka gabata, rundunar sojojin NATO dake karkashin jagorancin kasar Amurka ta kai wa jamhuriyar tarayyar Yugoslavia, wadda kasa ce mai mulkin kai hari daga sama ba tare da samun iznin kwamitin sulhun MDD ba, harin da ya haddasa mutuwar dubban fararen hula, ciki har da ‘yan jaridar kasar Sin guda uku. Al’ummun Sinawa ba za su manta da wannan danyen laifin da NATO ta aikata ba har abada. Kuma ba zai yiwu su yarda a sake aikata irin wannan laifin ba. Bangaren Serbia da ofishin jakadancin kasar Sin dake Serbia su kan shirya ayyukan tunawa da lamarin a kowace shekara.”
Kana rahotanni sun nuna cewa, kwanan baya shugaban Paraguay Santiago Peña Palacios ya gayawa manema labaran kasar Japan cewa, kungiyoyin aikin gona na kasarsa sun bukace shi da ya kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin, shugaban kasar Brazil Luiz Inácio Lula da Silva shi ma ya dade da gabatar da shawarar cewa, ya dace Paraguay ta kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin. Game da wannan, Lin Jian ya bayyana cewa, “Nacewa kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, matsaya ce da aka cimma a fadin duniya, muna fatan shugabannin kasashen da abin ya shafa su bibiyi tarihi kuma su bi burin al’ummomin kasa da kasa, haka kuma su yi zabin da ya dace, ta yadda za su tsai da kudurin da zai dace da babbar moriya mai dorewa ta kasashensu.” (Jamila)