Sanarwar hadin gwiwa ta Sin da Faransa game da yanayin yankin Gabas ta Tsakiya
2024-05-07 14:56:02 CMG Hausa
Tsakanin ranakun 5 zuwa 7 ga watan nan da muke ciki, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya kai ziyarar aiki kasar Faransa bisa gayyatar da shugaban kasar Emmanuel Macron ya yi masa. A yayin ziyararsa a kasar, shugabannin biyu sun yi musayar ra’ayoyi kan yanayin yankin Gabas ta Tsakiya.
A matsayin zaunannun mambobin kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin da kasar Faransa, sun hada kai wajen warware matsaloli, da fuskantar kalubalolin tsaro bisa dokokin kasa da kasa. Kaza lika kasashen biyu sun yi Allah wadai da dukkanin aikace-aikacen keta hakkin bil Adama, da kuma hare-haren da ake kaiwa fararen hula. Har ila yau, sun nuna adawa da aniyar kasar Isra’ila na kai hari birnin Rafah, kasancewar hakan zai haddasa mummunar bazaranar jin kai a yankin, kana sun yi Allah wadai da matakin tilastawa Falasdinawa yin kaura.
A daya bangaren kuma, shugabannin kasashen biyu sun jaddada cewa, abu mafi muhimmanci a halin yanzu, shi ne tsagaita bude wuta ba tare da bata lokaci ba, kana sun yi kira da a dawo teburin shawarwari, domin aiwatar da “daftarin kafa kasashe biyu” yadda ya kamata. Shugabannin Sin da Faransa, sun kuma jaddada matsayarsu, game da warware batun nukiliyar kasar Iran ta hanyar siyasa da diflomasiyya, da kare ’yancin zirga-zirgar jiragen ruwa kan bahar Maliya da gabar tekun Aden, da tabbatar da bin dokar tsagaita bude wuta a yayin gasar wasannin Olympics, da ajin gasar na nakasassu na lokacin zafi na shekarar nan ta 2024, wanda za a gudanar nan gaba a kasar ta Faransa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)