An rantsar da Putin a matsayin shugaban kasar Rasha a karo na 5
2024-05-07 21:00:35 CMG Hausa
Vladimir Putin, a lokacin da aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Rasha a yau Talata ya ce, Rasha za ta shawo kan dukkan cikas tare da cimma burinta na ci gaba,
Putin ya samu kashi 87.28 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar Rasha na 2024, wanda ya gudana daga ranar 15 zuwa 17 ga Maris.
An zabi Putin a matsayin shugaban kasar Rasha a ranar 26 ga Maris, shekara ta 2000, sannan aka sake zabarsa a karo na biyu a ranar 14 ga Maris, shekarar ta 2004. Daga 2008 zuwa 2012, ya yi aiki a matsayin firaminista.
Ya samu gagarumar nasara a zaben shugaban kasa na 2012 kuma an sake zabarsa a 2018 na tsawon wa’adin shekaru shida. (Yahaya)