Ibrahim Naziru: Za’a inganta samun hadaka tsakanin Sin da Najeriya a bangaren noma
2024-05-07 16:16:07 CMG Hausa
Ibrahim Naziru, ma’aikaci ne daga ma’aikatar gona ta tarayyar Najeriya. A halin yanzu yana wani karin karatu a kasar Sin, wato a birnin Handan dake lardin Hebei, domin kara kwarewa a fannin aikin gona.
A zantawarsa da Murtala Zhang, malam Ibrahim Naziru, wanda ya fito daga birnin Gusau na jihar Zamfara, ya bayyana bambancin yanayin karatu a bangaren noma tsakanin Najeriya da kasar Sin, da kuma yadda zai yi amfani da ilimin da ya samu a kasar Sin domin koyar wa manoman Najeriya ilimin zamani a bangaren noma.
Ibrahim Naziru ya kuma bayyana ra’ayinsa kan rayuwa mai sauki a kasar Sin, gami da yin kira ga mutanen Najeriya da su dage wajen neman ilimi da sana’a. (Murtala Zhang)