logo

HAUSA

Xi Jinping ya isa Tarbes na kasar Faransa

2024-05-07 18:25:24 CMG Hausa

Yau Talata, 7 ga wata bisa agogon wurin, shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwar gidansa Peng Liyuan sun iso birnin Tarbes, don ci gaba da ziyarar aiki a kasar Faransa. Takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron da uwar gidansa Brigitte Macron da ma wasu jami’an wurin sun tarbe su a filin jiragen sama.  (Bilkisu Xin)