logo

HAUSA

Xi ya halarci bikin rufe taron kwamitin ‘yan kasuwan Sin da Faransa karo na 6

2024-05-07 02:47:26 CGTN

A daren ranar 6 ga wannan wata, agogon Faransa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin rufe taron kwamitin ‘yan kasuwan kasashen Sin da Faransa karo na shida da aka gudanar a dakin wasan kwaikwayo na Marigny dake Paris tare da takwaransa na Faransa Macron, kuma ya gabatar da jawabi.

A cikin jawabinsa, Xi ya jaddada cewa, kasar Sin za ta kara bude kofa ga ketare a bangarorin sadarwa da kiwon lafiya, kuma za ta kara bude kasuwarta ga ketare domin samar da karin damammaki ga kamfanonin kasashen duniya, ciki har da Faransa, misali za ta shigo da kayayyakin aikin gona masu inganci daga Faransa domin kyautata rayuwar Sinawa. Ban da haka, kasar Sin ta tsai da kudurin tsawaita manufar soke biza na gajeren lokaci ga ‘yan asalin kasashe 12, ciki har da Faransa zuwa shekarar 2025.

Hakazalika, Xi ya bayyana cewa, kasar Sin tana shirin kara zurfafa kwaskwarima domin samar da babbar kasuwa da karin damammakin hadin gwiwa ga kasashen duniya. Kuma tana maraba da ‘yan kasuwan Faransa da suka halarci taron da su shiga kokarin da kasar Sin take yi wajen zamanantar da kasar, tare kuma da more damammakin kasar Sin. (Jamila)