logo

HAUSA

Shugaba Xi ya wallafa makalar da ya sanyawa hannu a jaridar kasar Serbia

2024-05-07 14:43:30 CMG Hausa

A ci gaba da ziyarar aiki da yake yi a wasu kasashen Turai, a yau Talata 7 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya wallafa makalar da ya sanyawa hannu a jaridar Politika ta kasar ta Serbia a jajibirin ya kai ziyararsa ta aiki a Belgrade.

Makalar ta shugaba Xi mai taken "Fatan hasken managarcin kawancen mu zai haskaka tafarkin hadin gwiwar Sin da Serbia", ta hakaito shugaban na Sin na bayyana cewa, wannan ne karo na biyu da zai kai ziyara a Serbia, kasa mai kyakkyawan muhalli da dogon tarihi, tun bayan da ya kama aiki a matsayin shugaban jamhuriyar jama’ar kasar Sin.

Ya ce duk da nisan dake tsakanin Sin da Serbia, kawancen dake tsakanin kasashen biyu na kara karfafa a tsawon lokaci, wanda hakan ya samar da wani kyakkyawan misali na musaya tsakanin kasashen da al’ummunsu. Kaza lika ya jaddada cewa, ta hanyar wannan ziyara, yana fatan yin aiki tare da bangaren Serbia, wajen ci gaba da yaukaka managarcin kawance tsakanin Sin da Serbia, da aiwatar da kyawawan matakai da za su amfani al’ummun sassan biyu, da ingiza zaman lafiya da ci gaban duniya, da hada gwiwa wajen gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama.

Shugaba Xi Jinping ya kara da cewa “Bai kamata mu manta da yadda shekaru 25 da suka gabata, dakarun tawagar NATO suka jefa bam a ofishin jakadancin Sin dake Yugoslavia ba. Al’ummun Sin na martaba zaman lafiya, amma ba za su bari mummunan abu da ya faru a tarihi ya sake maimaituwa ba. Kawance na jini da tsoka tsakanin Sinawa da al’ummar Serbia, ya zamo abu da a kullum sassan biyu ke tunawa da shi, wanda kuma zai ingiza sassan biyu wajen tunkarar ci gaban su tare. A shirye muke mu yi aiki tare da abokanmu na Serbia, wajen nacewa burikan mu na asali bisa gaskiya, kana za mu ci gaba tare, za mu bude sabon babin bunkasawa, da kara farfado da kasashen mu, da gina al’ummar Sin da Serbia mai makomar bai daya a sabon zamani. (Saminu Alhassan)